1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bam daya fashe a Indiya ya janyo mutuwar akalla mutane 11

September 7, 2011

An samu asaran rayuka da jikkata a wani mummunan harin bam da aka kai a harabar wani kotu da ke birinin New Delhi babban birnin ƙasar Indiya

https://p.dw.com/p/12UD1
Wani da ya jikkata a harim bam na yau a New DelhiHoto: dapd

Aƙalla mutane 11 ne suka mutu kana wasu kimanin 76 kuma suka sami rauni sakamakon wani bam da ya tarwatse a babbar kofar shiga wata kotun tarayya dake birnin New Delhi na kasar Indiya. A cewar wani kwamishinan 'yan sanda na musamman a ƙasar ta Indiya Dharmendra Kumar bam ɗin da ya fashe a safiyar yau Laraba, ga dukkan alamu an sanya shi ne a cikin wani ƙaramin akwati kusa da wurin karbar baƙi a ɗaya daga cikin manyan kofofin shiga cikin kotun.

Babu dai wata ƙungiyar da ta ɗauki alhakin ƙaddamar da harin, wanda ke zama mafi muni cikin tsukin watanni biyu, bayan tagwayen bama-baman da suka janyo mutuwar aƙalla mutane 24 a Mumbai, babban birnin kasuwancin ƙasar ta Indiya. Kasancewar mazaunin kotun da bam ɗin ya fashe yana kusa da majalisar dokokin ƙasar ta Indiya, kana babu tazara sosai da ofishin firai ministan ƙasar, ya sanya ayar tambaya akan sha'anin tsaro a ƙasar, ko da shike kuma a cewar jami'in kula da harkokin tsaron cikin gida a ma'aikatar cikin gidan Indiya U. K. Bansal tuni hukumomi suka tsaurara matakan tsaro a yankin da lamarin ya afku dama ɗaukacin birnin New Delhi bayan fashewar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Usman Shehu Usman