Ban ya yi kira da dakatar da rikicin Gaza
August 6, 2014Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon, yayi kira a wannan Larabar da a dakatar da halin muzgunawar da ake yi a Zirin Gaza. Ban ya yi wannan furuci ne cikin wani jawabi da ya yi a gaban babban taro na Majalisar da kasashen Larabawa suka kira kan batun na Gaza, inda ya kara da cewa haka za a ci gaba, a gina kuma a rushe, kuma a sake ginawa? Wannan ita ce ayar tambayar da Ban Ki Moon din ya yi, sannan ya kara da cewa za su sake gina Gaza amma kuma ya kyautu hakan ta zamanto na karshe.
Mista Ban ya kara da cewa, ya kyautu wannan yarjejeniyar tsagaita wutar ta kwanaki ta kai ga samun tsagaita wuta na dindindin. Kuma ta kai ga magance dalilan da suka haifar da rikicin, kamar batun kange Gaza da Isra'ila ta yi, tare da sanya al'ummar Gaza cikin dunkulalliyar gwamnati ta Falasdinu wadda za ta yi biyayya ga muradu na gamaiyar kasa da kasa.
Mawallafi: Salisosu Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal