Banbanci tsakanin EFCC da ICPC
October 1, 2012EFCC dai hukuma ce da ke mahukuntan Najereiya su ka bijiro da ita domin yai da yiwa tattalin arzikin ƙasa ko kuma wani mutum ta'annati gami da yaƙi da masu halasta kuɗin haram. Kazalika doka ta ba EFCC damar hukunta masu safarar kuɗi daga wannan ƙasa zuwa wata.
Hukumar ICPC a nata ɓangaren an ƙirƙire ta ne domin ta yaƙi da cin hanci da kuma karɓar rashawa a wani yunƙuri da mahukuntan na Njeriya ke yi na ganin waɗannan munanan ɗabi'u sun zama tarihi a ƙasar.
A nan a iya cewa bambancin da ke akwai tsakanin hukumomin biyu shi ne EFCC ta fi maida hankali kan yi wa tattalin arziƙi ta'annati ko dai na hukuma ko kuma na wani mutum yayin da ICPC a nata ɓangaren ta fi karkata ga batun cin hanci da rashawa. Sannan ICPC ɗin har wa yau na taimakwa jami'an 'yan sanda wajen batun yaƙin da su ke na cin rashawa.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou