1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bangladesh: 'Yan adawa na yajin aiki gabanin babban zabe

January 6, 2024

Babbar jam'iyyar adawa ta kasar Bangladesh ta fara yajin aikin gama-gari na tsawon sa'o'i 48, kwana guda gabanin babban zaben kasar.

https://p.dw.com/p/4avr4
Shirye-shiryen zabe a kasar Bangladesh
Shirye-shiryen zabe a kasar BangladeshHoto: Mohammad Ponir Hossain/REUTERS

Jam''iyyar ta bukaci al'ummar kasar da su kauracewa kada kuru'a sakamakon rashin tabbacin da take da ita kan gwamnatin Firanminista Sheikh Hasina na yin adalci. Hasina dai na neman sake yin tazarce kan madafun ikon kasar a karo na hudu.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, 'yan adawa sun yi tattaki a wannan Asabar din a babban birnin kasar Dhaka domin kira ga mutane su shiga yajin aiki tare da mika bukata ga shugaba Hasina da ta yi murabus. Tuni dai hukumar zabe ta kasar ta ce ta fara raba kayayyakin zabe a mazabu fiye da dubu 42, kana ta bukaci a kara yawan jami'an tsaro a runfunan zabe.

Karin bayani: An kashe masu zanga-zanga a Bangladesh

Kawo yanzu dai hukumomi na cewa, an kama wasu 'yan jam'iyyar BNP hudu da ake zargi da hannu wajen kai wani hari a jirgin kasa a jiya Juma'a wanda ya yin sanadiyar mutuwar fasinjoji hudu.

An dai fuskanci tashe-tashen hankula yayin yakin neman zabe a kasar mai yawan al'umma komanin miliyan 169, inda mutane 15 suka mutu tun daga watan Octoba. Bangladesh dai na bin tafarkin dimokradiya ne sai dai kuma, kasar na da tarihin juye-juyen mulki.