SiyasaBangladesh
Sheik Hasina na shirin fuskantar hukunci
December 23, 2024Talla
Sheik Hasina, wacce ta mulki Bangladesh da sandar karfe, wadda gwamnatinta ta rika samun goyon bayan New Delhi, ta arce zuwa Indiya da jirgin sama mai saukar ungulu a ranar biyar ga watan Agusta lokacin da masu zanga-zangar suka mamaye fadar firayim minista a Dhaka, bayan shafe makonni suna yin borai. A tsawon shekaru 15 na mulki ana zarginta da keta hakin dan Adam tare da kulle jamaa da dama a gidan yari da yin kisa barkatai kan yan adawa.