Bankin duniya ya damu kan koma bayan ilimi a Najeriya
October 21, 2013Bankin duniya da reshen ofishinsa da ke Najeriya ya bayyana cewar akwai matikar damuwa dangane da yadda yawan wadanda basu iya karatu da rubutu ba a Najeriya ke karuwa, kuma bankin ya nunar da dimbin kalubale na rayuwa da ke fuskantar 'yan kasar duk kuwa da dimbin arziki da aka san Najeriyar na da shi. Bankin na duniya dai yace ya zabi jihohi uku a kasar don amfana da wani bashin miliyoyin daloli da ke da nufin tallafar harkokin ilmi, ciki kuwa har da Jihar Anambra.
Bankin na duniyar dai ya nunar cewar kimanin 'yan Najeriya miliyan 40 ne da ke tsakanin shekaru 15 zuwa sama a yanzu ke fama da matsalar rashin iya karatu da rubutu na boko, kuma wannan adadi yana kan karuwa ne, sannan kuma tace yanayin abin damuwa ne matika, domin yanzu kasar ta Najeriya ta shiga sahun wasu kasashe goma na duniya da ke da matsalar yawan jama'ar da basu san bihim ba a ilmin boko.
Bankin na duniyar dai ya bayyana wannan yanayi na koma-baya a ilmi ne a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriyar a baya bayannan yayin bayyana wani bashin dala miliyan 150 da jihar ta Anambra, gami da Jihohin Bauchi da Ekiti za su amfana, wadda ke cikin shirin bankin na zuba jari a harkokin ilmi da nufin inganta harkokin ilmi a jihohinnasu, shirin kuma da ke da hadin gwiwar gwamnatin Tarayyar Najeriya. Mr. Mike Uda shine mai magana da yawun gwamnan jihar ta Anambra,na kuma same shi ta waya,ga kuma abainda yake cewa:
"Mr Uda yace wadannan kudade da jihar Anambra za ta karba za ta sarrafa sune kamar yadda ta saba a cikin tsare-tsarenta na ciyar da jihar gaba ,don ganin cimma kudurorin da ke cikin shirin raya kasa na MDG da ayyukan habaka ilmi kuma na ciki. Kuma Gwamnatimmu na da kyakkayawan tarihi a kokarin ayyukan raya kasa. Kuma irin tsarin da muke da shi a kasa,wadda kuma bankin na duniya ya karanta, ina ganin shine ya baiwa jiharmu nasara wajen amfana daga wannan bashi na bankin, kuma babu makawa za muyi amfani da kudaden don ganin an samu mahimmin ci gaba a ilmi a jiharmu ta Anambra."
Yayin dai gabatar da jawabi a sa'ilin bayyana wannan shiri na bankin na duniya, wakilin bankin a Najeriya Mr. Sateh El Arnaoyi ya nunar cewar za a samu ingantaccen ci gaba ne kawai a kasar in har gwamnati ta maida hankali wajen zuba jari na kudade sosai a harkokin ilimi, inda ma har bnkin na duniya ya bayyana takaicin yadda jami'oi a Najeriya ke ci gaba da zama a rufe kusan watannin hudu yanzu, sakamakon yajin aiki da ke da jibi da halin tabara da jami'oin suka shiga.
Haka kuma bankin na duniya ya kara bayyana cewar,abin takaici ne matika ganin cewar kimanin kason 'yan Najeriya 46 ne cikin dari ke cikin katutun talauci ,ba a da bayan rashin adalci da ke gudana ga jama'ar kasar.
Kan batun matsalar rashin iya karatu da rubutu da kimanin mutane miliyan 46 a Najeriyar ke fuskanta, ga wasu 'yan kasar da basu je makarantar ta boko ba, amma dai sun nunar da kokarin da suke yi a sakamkon kalubale na rayuwa.
Kan bashin kudaden na bankin duniya, ministan ilmi na Najeriya Mr. Nyeson Wike ya tabbatar da cewar, maaikatar ilimi ta kasa za ta bi diddigi don kulawa da yadda wadannan jihohi uku da suka samu kudaden na bankin duniya za su sarrafa su, don tabbatar da cewar an kashe kudaden bisa manufofi da sharuddan da aka gindaya.
Bankin na duniya dai ya tabbatar da kudirinsa na tallafawa a fannonin samar da kudade da kayan aiki don ci gaban al'umma,da tabbatar da cewar wadanda ya kamata su je makaranta na zuwa makaranta da tabbatar da samar da isassun malaman makaranta, sannan da bin diddigin yadda al'ammura ke gudana ga dukkaninn jihar da ta sa jarinta don habaka ilimi din.
Mawallafi: Muhammad Bello
Edita: Umaru Aliyu