1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankin Duniya ya ware kudin yakar Ebola

August 5, 2014

Makudan kudade hukumomin kudi na Afirka da na duniya suka ware don ja wa cutar Ebola da ta fi addabar kasashen yammacin Afirka birki.

https://p.dw.com/p/1Cp88
Hoto: Reuters

Bankin Duniya ya ware kudi miliyan 150 na Euro don yakar cutar Ebola da ke hallaka bayin Allah a kasashe da dama na yammacin Afirka. Daga cikin wadanda za su ci gajiyar wannan kudi har da Hukumar Lafiya ta Dunuiya da kuma kasashen Gini Conakry da Liberiya da Saliyo inda cutar ta fi yaduwa.

Alkaluma sun nunar da cewar mutane 900 suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Ebola tun bayan bullarta a watan Fabrairu, yayin da wasu karin mutane 1600 ke dauke da kwayar cutar a halin yanzu.

Ebola dai na ci gaba da bazuwa a duniya inda a baya-bayan nan hukumomin Najeriya suka ce likitan da ya duba dan kasar Liberiyan nan mai dauke da cutar Ebola a jihar Lagos ya kamu da ita. Kungiyar kasa da kasa ta Medecins sans Frontieres ta bukaci kasashen da abin ya shafa da daukan matakan rigafi don hana yaduwarta tsakanin al'umma. Babu dai wani rigakafi ko kuma maganin Ebola da aka samu ya zuwa yanzu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal