Bankin duniya zai zuba jari a Afirka
March 20, 2017Bankin dai ya bayyana wannan kudiri ne a yayin taron ministocin kasashe masu karfin tattalin arziki na n G20 na da kasashen Afirka da ya gudana a Jamus. Cikin wata sanarwa shugaban Bankin Duniyar Jim Yong Kim ya nunar da cewa, daga cikin wannan kudi, za a bayar da dalar Amirka miliyan 45,000 ta hanyar kungiyar raya kasashe ta kasa da kasa wadda ke matsayin wani reshe na Bankin Duniyar, da ke bayar da tallafi da kuma basussuka ba tare da ruwa ba ga wasu kasashe matalauta. Za kuma a yi amfani da dalar Amirka miliyan 8,000 ta hanyar karamar cibiyar Bankin Duniya ta IFC, sannan sauran dala miliyan 4,000 kuma su isa ta hanyar bankin kasa da kasa na sake gini da bunkasa kasashe na BIRD, wanda shi ma wani reshe ne na Bankin Duniyar.
Kasar Jamus dai da ta karbi bakuncin babban zaman taron ministocin kasashe 20 masu karfin masana'antu wato G20, ta sanar da aniyarta ta kara karfafa huldar da ke tsakaninta da kasashen Afirka a wannan shekara ta 2017.