1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zambiya ta yi bankwana da gwarzonta

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 2, 2021

Masu zaman makoki dauke da fararen kyalle da ke alamta taken marigayi tsohon shugaban kasar Zambiya Kenneth Kaunda sun yi bankwana da shi, yayin jana'izarsa da aka gudanar a hukumance a Lusaka.

https://p.dw.com/p/3vxka
Kenneth Kaunda | ehemaliger Präsident Sambias
Hoto: Stephane De Sakutin/AFP/Getty Images

Kaunda da ke zaman shugaban kasar Zambiya na farko, ya rasu a ranar 17 ga watan Yunin da ya gabata yana da shekaru 97 a duniya bayan ya sha fama da cutar Limoniya. Kaunda da ke zaman jagoran gwagwarmayar kwatar 'yanci a Afirka guda daya tilo da ya yi tsawon kwana, ya fara yawo da farin kyalle ne da kullum yake tare da shi bayan da ya fara fafutukar nemawa kasarsa 'yanci daga hannun Turawan mulkin mallaka na Birtaniya, farin kyallen da ya bayyana da cewa yana alamta soyayya da zaaman lafiya. An dai gudanar da jana'izar ne cikin bin ka'idojin yaki da annobar coronavirus da ta addabi duniya, annobar kuma da ba ta hana shugabannin Afirka da jami'an diplomasiya isa birnin Lusaka fadar gwamnatin Zambiyan domin yin bankwana da shi ba.