Baraka kan jingine nukiliyar Koriya ta Arewa
May 17, 2018Talla
Koriya ta Arewa ta ce za ta iya janyewa daga zaman da aka shirya a tsakanin shugaba Kim Jung-un da takwaransa Donald Trump, muddun Amirka ta ci gaba da matsa ma ta da wasu sharudda kan lalata tashoshin nukiliyar baki daya, duk da cewa Amirkan a na ta bangaren ta yi alkwarin fitar da sunan kasar daga cikin jerin sunayen kasashe masu tallafawa ayyukan ta'addanci a duniya.
Kawo yanzu dai akwai shakku dangane da taron Koriya ta Arewar da Amirka a wata mai kamawa, biyo bayan atisayen da sojin Amirkan suka yi a Koriya ta Kudu, wanda Pyongyang ta bayyana a matsayin tsokana, tare da soke ganawar manyan jami'an bangarorin biyu.