1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yiwuwar kai hari a Afghanistan

Abdoulaye Mamane Amadou
August 29, 2021

A daidai lokacin da kasashen duniya suka dakatar da jigilar baki da masu neman tsira daga Afghanistan, Amirka ta ce akwai yiwuwar kai wani karin harin ta'addanci Kabul.

https://p.dw.com/p/3zd6L
Afghanistan| ein US-Militärflugzeug startet am Flughafen in Kabul
Hoto: Wali Sabawoon/AP/picture alliance

Shugaban Amirka Joe Biden ya bayyana fargabar yiwuwar kaddamar da wani mummunan harin ta'addanci yau ko gobe a birnin Kabul, kwana daya bayan da dakarun tsaron Amirkar suka hallaka wasu kusoshin kungiyar IS K biyu da jirgi maras matuki da aka zarga da kitsa harin birnin Kabul.

Shugaba Biden ya ce cikakkun bayanai daga sojan kasar sun kwarmata cewa akwai yiwuwar sake kai wani mumunan hari nan da sa'o'i 24 zuwa 36 da ke tafe.

Tuni dai hukumomi kasar a Afghanistan suka gargadi 'yan kasar da su kauracewa zuwa filin jirgin Kabul, suna masu cewa barazanar kai harin ta fi kamari ne a kofar filin jirgin Kabul ta Kudu da ma'aikatar tsaron Afghanistan hakan da wata kofar  Panshir da ke arewacin filin jirgin da tafi kusa da wani gidan mai.