1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar masana'antu kan muhalli

May 5, 2017

Matsalar sauyin yanayi na ci gaba da zama barazana ga manyan kasashen duniya musammam wadanda ke da karfin masana'antu masu sarrafa kayayyakin da ake amfani da su na yau da kullum. 

https://p.dw.com/p/2cU2B
Masana'antu na taka rawa wajen gurbata muhalli
Masana'antu na taka rawa wajen gurbata muhalliHoto: Getty Images/E. Wray

Kafa masana'antu masu sako gurbatacciyar iska da adadin mutane da ke karuwa a doron kasa da tsarin rayuwa da ya canza, na daga cikin abubuwan da ke haifar da fargaba game da haifar da mummunan sakamako na dumamar yanayi.  A nahiyar Afirka kasar Ghana na daya daga cikin kasashen da ke sahun gaba da kokarin wayar da kai da kuma kiyaye duk abubuwan da ke iya janyo dumamar da yanayi ke yi. Rex Gyechie na cibiyar dumamar yanayi a jami'ar kasar Ghanan ya ce a halin yanzu akwai wasu kayan abinci da ba za a iya shuka su ba nan gaba, kamar ganyen koko da ke zama amfanin gona da yake rike da tattalin arzikin wannan kasa. 

Daya  daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne yanda kasashe za su dai-dai ta al'amuransu tare da rungumar matsalolin dake tattare da dumamar yanayi cikin sauki.  A kasar Ghana za a iya cewa aikin fadakar da jama'a bai yi nisa ba, amma manyan tarurrukan da kasar ke halarta a kasashen waje na yin taimako kwarai wajen zaman kasar cikin shirin ko ta kwana.