Barcelona ta yi raga-raga da Real Madrid
March 21, 2022an kara wannan wasa a filin wasa na Santiago Bernabéu Stadium da ke daukan mutane 81,000, kuma milyoyon 'yan kallo daga kasashe suka kalli wannan wasa mai tasiri. Sannan Espanyol ta doke Mallorca 1 mai ban haushi, kana Atletico Madrid ta yi Rayo Vallecano gida ta lallasa ta 1 da nema, yayin Sevilla da Real Sociedad suka tashi babau wadda ta jefa kwallo a raga.
A teburin na la Liga adda tsarin yake:
1 Real Madrid maki 66
2 Sevilla 57
3 Barcelona 54
4 Atlétic 54
5 Betis 50
A wasan Premier League na Ingila, Arsenal ta bi Aston Villa ta doke ta 1 da nema. Sannan Tottenham ta doke West Ham 3 da 1
A wasannin Bundesliga na Jamus, kungiyar Mainz ta doke Arminia 4 da nema, haka ita ma Bayern Munich ta doke Union Berlin 4 da nema, sannan Hertha Berlin ta doke Hofffenheim 3 da nema, yayin da Leverkusen ta bi Wolfsburg gida ta doke ta 2 da nema. Ana ta bangaren kungiyar Greuther Fuerth ta tashi babu jefa kwallo a raga da Freiburg. Kuma wasan da kungiyar Stuttgart ta doke Augsburg 3 da 2 muka kawo muku kai tsaye daga nan Sashen Hausa na DW, inda na gabatar da sharhin tare da Ramatu Garba Baba.
A teburin Bundesliga ga shima yadda tsarin yake
1 Bayern München maki 63
2 Dortmund 57
3 Leverkusen 48
4 Leipzig 45
5 Freiburg 45
A kasar Amirka lamuran wasannin na ci gaba da farfadowa bayan matakan annobar cutar coronavirus da duniya ta fuskanta.