Jirgin da ke dauke da shugaban Iran ya yi batan dabo
May 19, 2024Jirgi mai saukar ungulu da ke dauke da shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya yi batan dabo da yammacin ranar Lahadi kamar yadda kafar yada labaran Iran ta bayyana.
Shugaba Raisi na komawa ne daga wani yanki na gabashin kasar Iran da ta yi iyaka da Azerbeijan, bayan ziyarar kaddamar da wata madatsar ruwa da za ta amfani kasashen biyu.
Karin bayani: Kaucewa ta'azzarar rikicin Gabas ta Tsakiya
Gidan talabijin mallakar gwamnatin Iran ya ruwaito cewa lamarin ya auku ne a garin Jolfa dake iyaka da kasar ta Azerbeijan.
A cikin tawagar ta shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, har da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian da gwamnan lardin Azerbaijan na gabashin Iran da kuma wasu manyan jami'ai da ke kare lafiyarsu.
Babu wanda ya san halin da shugaban da tawagarsa ke ciki ya zuwa yanzu, masu aikin ceto ke ci gaba da neman jirgin duk kuwa da rashin kyawon yanayi a yankin.
karin bayani: An kama wadanda ake zargi da hare-hare a kasar Iran
Shugaban Azerbeijan Ilham Aliyev ya nuna damuwa matuka kan wannan labarin na bacewar jirgin mai saukar ungulu da ke dauke da shugaban Iran Ebrahim Raisi.