1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun cin hanci da rashawa a kasar Kenya

Ibrahim SaniFebruary 14, 2006

Harkokin cin hanci da rashawa a kasar kenya ya fara daukar sabon salo

https://p.dw.com/p/Bu1k

Ya zuwa yanzu dai abin da yafi daukar hankali a kasar ta Kenya shine batu na murabus da wasu ministoci biyu a gwamnatin shugaba Wmai Kibaki suka yi a jiya litinin.

Murabus din ministan ilimi, wato George Saitoti da ministan makamashi,wato Kiraitu Murungi, ya biyo bayan zargi ne da ake musu cewa suna da hannu a cikin wata almundahanar da aka tafka ta wasu miliyoyin daloli a kasar ta Kenya.

A misali bayanai sun nunar da cewa an zargi ministan ilimin ne da hannu a cikin wata ta´asa ta miliyoyin daloli da aka tafka ta hanyar hada hadar zinare da lu´u´lu´u, wacce aka fi sani da suna Goldenberg a turance.

Shi kuwa, ministan makamashin ana zargin sa ne da awon gaba da wasu makuden kudade ta hanyar biyan wani kamfanin bogi miliyoyin daloli bisa hujjar gudanar da wasu aiyuka a cikin wani shiri mai suna Anglo Leasing.

Kafin dai murabus din wadannan jami´ai manya manyan jami´an gwmnati uku ne suka bar mukaman su bisa zargi da ake musu da batu na cin hanci da rashwar.

Ya zuwa yanzu dai da yawa daga cikin jamiyyun adawa da yan jaridu da kungiyoyi masu zaman kansu sun yaba da wannan mataki da ministoci biyun suka dauka da cewa wata alama ce dake nuni da irin ci gaba da kasar ta samu a fagen harkoki na siyasa.

Bugu da kari yan kasar na kuma jiran ganin wasu jami´an gwamnatin da aka ambaci sunayen su a cikin rahoton binciken irin ta´asar da aka tafka a cikin wadannan batutuwa guda biyu ta hanyar yin murabus daga mukaman nasu.

Rahotanni sun shaidar da cewa da yawa daga cikin alummar kasar na nan na jiran irin matakin da gwamnati zata dauka akan mutanen da aka samu nada hannu a cikin wannan ta´asa da aka tafka, don yanke musu hukuncin daya dace.

Daukar wani kwakkwaran mataki a cewar su shine zai tabbatar da irin ikirarin da shugaba Wmai kibaki keyi na dakile batu na cin hanci da rashawa a kasar, kamar yadda ya fadi hakan a tun darewar sa karagar mulki.

Bayanai dai daga kasar a yanzu haka sun tabbatar da cewa tuni jami´an yan sandan kasar suka umarci wasu mutane 20 da ake bincike dasu mika takardun fasspo nasu, a waje daya kuma kungiyoyi masu zaman kansu sun shaidar da gudanar da gudanar da wata gagarumar zanga zanga a ranar juma´a mai zuwa don bayyana ra´ayin su na a ci gaba da yaki da wannan mugunyar cuta.

A wata sabuwa kuma, yan majalisar dokokin kasar daga jamiyyun adawa sun bukaci majalisar data koma zaman ta don fara tattauna wannan batu na cin hanci da rashawar.

Idan dai za a iya tunawa a watan nuwambar bara ne shugaba Wmai Kibaki ya dakatar da zaman majalisar, a sakamakon kaye daya sha a zaben raba gardama na gudanar da yan gyare gyare a cikin kundin tsarin mulkin kasar.