Bayern Munich za ta karbi dan wasan Manchester City
May 6, 2020Talla
Hakan zai faru ne a karkashin wani tsari na musanya. Leroy Sane dan asalin kasar Jamus ya jima bai taka leda ba tun a watan Agustan da ya gabata bayan da ya samu rauni a gwiwarsa.
Sai dai rahotanni sun ce har yanzu ba su daddale a kan ko nawa Bayern Munich za ta biya Manchester City a kan wannan musaya ba. Amma dai wasu na cewa ko nawa aka ba Manchester City za ta karba tun da a yanzu tana cikin matsalar rashin kudi saboda annobar coronavirus.
Wannan musaya dai na zuwa ne yayin da a wannan Laraba gwamnatin Jamus da gwamnoni 16 na jihohin kasar ke ganawa don duba yiwuwar bude wasannin Bundesliga a cikin wannan wata.