1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bayyana sakamakon zaben Kenya ya bar baya da kura

March 9, 2013

Raila Odinga da ya fafata da Kenyatta a zaben shugaban kasar Kenya ya bayyana kudirin kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotu.

https://p.dw.com/p/17uLW
President elect Uhuru Kenyatta displays the certificate from Independent Electoral and Boundaries Commission (IEBC) declaring him the winner of the country's general election in Nairobi March 9, 2013. Kenyatta, indicted for crimes against humanity, was declared winner of Kenya's presidential election on Saturday with a tiny margin, just enough to avoid a run-off after a race that has divided the nation along tribal lines. REUTERS/Noor Khamis (KENYA - Tags: ELECTIONS POLITICS)
Hoto: Reuters

Zababben shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya bukaci abokin hamayyarsa a zaben shugaban kasar daya gudana a ranar Litinin da ta gabata, wato Raila Odinga da ya bashi goyon baya domin gudanar da ayyukan da za su inganta rayuwar daukacin al'ummar Kenya. Mr. Kenyatta ya bayyana hakan ne jim kadan bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Shugaban kasar Kenya na gaba Uhuru Kenyatta ya bayyanawa 'yan Kenya maza da mata cewar yana nuna tawa'liunsa na ganin cewar a zaben daya gudana cikin 'yanci da walwala ne suka mika masa ragamar jagorancin kasar a matsayin shugabansu na gaba.

Mr. Kenyatta ya ce babban abinda zai sanya a gaba - da zaran an rantsar da shi a matsayin shugaban Kenya shi ne yin aiki tukuru domin cika alkawuran daya dauka a lojacin yakin neman zabe da kuma inganta harkokin zaben kasar domin gujewa kura-kuran da aka samu a shirin zaben, wanda ya ce duk da haka ya sa kasar Kenya tabbatarwa duniya cewar tana bisa kyakkyawar turbar wanzar da dimokradiyya a kasar:

Ya ce " Duk da tababar da wasu da dama suna nuna a wasu sassa na duniya, mun tabbatar da cewar mun ci gaba sosai a sha'anin siyasa fiye da yanda ake zato."

Kenya's Prime Minister and presidential candidate Raila Odinga gives an interview to AFP on January 14, 2013, in his office in Nairobi. Kenya is less than two months away from the first presidential elections since deadly post-poll violence five years ago. While two main candidates -- Uhuru Kenyatta and Raila Odinga -- dominate the race, all six candidates have potential influence, especially if voting goes to a second round run off after the March 4 vote. AFP PHOTO/SIMON MAINA (Photo credit should read SIMON MAINA/AFP/Getty Images)
Raila OdingaHoto: Getty Images/AFP

'Yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaben Kenya

Mr Uhuru Kenyatta ya kuma yabawa babban abokin hamayyarsa a zaben, wanda kuma ke zama firayiministan kasar Raila Odinga bisa abinda ya ce kyakkyawan salon yakin neman zaben daya gudanar, inda ya bukaci ya zo ya hada kai dashi domin ci gaban Kenya, ko da shike kuma bangaren Raila Odinga ya bayyana kudirin kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotu.

Tunda farko dai shugaban hukumar zaben Kenya Issack Hassan ya sanar da cewar bayan kidaya kuri'un da aka jefa, Uhuru Kenyatta ne yayi nasara a zaben:

Ya ce " Tunda Uhuru Kenyatta ne ya sami kuri'u miliyan 6 da dubu 173 da 433, kenan ya sami fiye da kashi 50 cikin100 na daukacin kuri'un, wanda akan hakane kuma nake bayyana shi Uhuru Kenyatta a matsayin halattaccen zababben shugaban Kenya."

Judges of the International Criminal Court Akua Kuenyehia, president Claude Jorda and Sylvia Steiner, top left to right, are seen at the start of a hearing in The Hague, Netherlands, Thursday, Nov. 9, 2006. The ICC opened a hearing to consider evidence against alleged Congolese warlord Thomas Lubanga, accused of recruiting child soldiers, a landmark first case for the permanent war crimes tribunal. Lubanga, the only suspect in the court's custody, is accused of recruiting child soldiers and using them to kill and mutilate his enemies. The hearing is meant to determine whether the evidence against Lubanga is strong enough to merit a full trial. ( AP Photo/ Bas Czerwinski)
zaman kotun ICCHoto: AP

Makomar Kenyatta a gaban kotun ICC

Sai dai kuma shugaban na Kenya mai jiran gado Kenyatta, harma da mutumin da ke rufa masa baya wato William Ruto na fuskantar zargin aikata manyan laifukan yaki a gaban kotun duniya ta ICC da ke birnin The Hague na kasar Holland, bisa zargin suna da hannu a rikicin kabilancin daya biyo bayan zaben kasar a shekara ta 2007, wanda ya janyo mutuwar kimanin 'yan Kenya 1,200, wanda kuma ya sa wasu kasashen duniya nuna tababar yin aiki tare da shi a irin wannan yanayi, amma a yanzu Kenyatta ya yi alkawarin gujewa nuna banbancin addini ko na kabilanci yayin gudanar da aikinsa, kana da bayyana kudirin bayar da goyon bayansa ga kotun a shari'ar da take yi masa.

Tuni dai wasu manazarta ke yin kira ga baiwa Kenyatta goyon bayan da ya ke bukata domin mutunta zabin da 'yan Kenya suka yi.