Bazoum: Tarukan Lumana ba su cika ka'ida ba
September 27, 2019An jima ana jiran yadda za ta kaya dangane da bangaren da zai yi nasara a babban zaman taro na jam’iyyar adawa ta Lumana Africa wanda aka yi daya a birnin Dosso, daya a birnin Yamai, inda kowane bangare ke kurin shi ke da gaskiya. A halin yanzu dai ta tabbata cewa ofishin ministan cikin gida ya yi hatsi da tarukan biyu na Jam’iyyar Lumana Afrika ta Hama Amadou, inda ya ce bayan dogon bincike da kwararrun ma'aikatar cikin gidan suka yi, sun gano cewa taron da aka yi a Dosso shi ne aka yi a kan ka’ida, domin shugaban riko na jam’iyya shi ne wanda ya kira taro a Dosso. Sai dai kuma ganin cewa taron na Dosso bai samu adadin wakillan da suka dace ba, ba zai samu halarci ba.
Yayin da aka kai ga takardun wadanda suka yi nasu taro a birnin Yamai, wadanda kuma ke buga gaban cewa taronsu ne ya samu mafi yawan wakillan da suka kamata su halarci taron na Congres, takardar ofishin ministan cikin gidan kasar ta Nijar wadda magatakardanta Ider Adamou ya sa wa hannu, ta ce lalle wadanda suka yi taro a Yamai ba su da wannan hurumi na yinsa, domin kuwa takardar da shugaban riko da na jam’iyyar wanda shi ne ke da izinin kiran taro ya aike, ta ce a Dosso ne za a yi taron na Congres don haka yin taro a Yamai bai kasance cikin ka’idar da za a bada halarcin taron ba.
Masu sharhi na fadar cewa wannan dai wata dama ce ta jam’iyyar Lumana Afrika da mambobinta suka samu na dinke barakar da ke neman watsa jam’iyyar, inda ake ganin idan da kowane bangare zai cire son kai, to da za a samu mafita tare da sake dunkulewa a matsayin tsintsiya madaurinki daya.