Bazuwar 'yan Jahadi a yakin Siriya
September 19, 2013Yakin basasan kasar Siriya na ci gaba da janyo masu kaifin kishin addinin Islama, wadanda ke shiga domin aiwatar da manufar Jahadi. Tuni 'yan Jahadin suka mamaye rundunonin 'yan tawaye cikin sassa daban-daban na kasar. Inda aka bayyana cewa a yanzu dubban masu ikirarin Jahadi daga kasashen duniya suka kwarara domin tallafa wa 'yan adawa da ke neman kifar da gwamnati shugaba Bashar al-Assad.
Michael Stephens dan kasar Birtaniya na cikin wata kungiya mai zaman kanta, wadda ke kula da abin da ke faruwa cikin kasar ta Siriya, musamman yadda 'yan jahadi ke mamaye rundinonin 'yan tawaye:
"Ina ganin akwai kimanin mayakan Islama 60.000, kuma kimanin 2,000 zuwa 3,000 ne abin tsoro, wadanda su ke da tsananin ra'ayi da za a nuna damuwa. Amma kuma wannan adadi na 2,000 zuwa 3,000 abu ne mai yawa"
Mafi yawan wadan nan mayaka na Jahadi da ke kai gudumawa cikin yakin basasan kasar ta Siriya, sun fito ne daga kasashen ketere. Michael Stephens ya yi karin haske kan yankunan da wasu daga ciki su ka fito:
"Mun san cewa daruruwa sun fito daga arewacin Turai, akwai shaidar cewa wasu sun fito daga birnin Hamburg na arewacin Jamus, wasu daga kasar Denmark, da ga Sweden, da ga Holland inda ake tura mutane da sunan kungiya. Suna haduwa a kudancin kasar Turkiya, daga nan suke shiga biranen Siriya na Aleppo ko Idlib"
Daya daga cikin kungiyoyin da ake tsoro kuma ake dangantawa da kungiyar al-Ka'ida, ita ce Al-Nusra. Ana daukan kungiyar a matsayin mai nuna rashin imani. Michael Stephens ya ce 'yan kungiyar tsiraru ne cikin rikicin.
"Kididdiga ta nuna yawan 'yan kungiyar Al-Nusra sun kai 5,000. Ina tsammani adadin na da yawa"
Rikicin kasar ta Siriya na kara zafafa, inda masu ikirarin Jahadi ke kai ruwa rana da dakarun gwamnati masu biyayya ga mahukuntan birnin Damascus.
Paul Salem daraktan wata gidauniya ta Gabas ta Tsakiya, ya yi bayani kan dangantaka tsakanin 'yan Jahadin da mazauna garuruwan kasar.
"Babu wani tsaro, mazauna garuruwan sun amince da masu kaifin kishin addinin, ko sun saba da masu neman kafa sharia irin na Wahabiyawa. Da kafa tsarin kama-karya, shugaban tsagerun ke zama alkali, wajen aiwatar da shari'a, kamar yanke hanun ko fille kai, ta mummunar hanya"
Cikin wannan rikici na Siriya 'yan tawaye na samun tallafi daga kasashen Yammacin duniya, wadanda kiri-kiri suke nuna adawa da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad. Kungiyar Free Siriya tana cikin kungiyoyin da ke samun tallafi, wanda kuma ke dasawa da kasashen na Yammacin duniya. Wadannan 'yan tawaye kan samu kudi da makamai da sauran kayayyakin da suke bukata, daga kasashe masu nuna adawa da gwamnatin kasar. Yayin da kasashe kamar Rasha da Iran ke ci gaba da goyon bayan gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.
Mawallafa: Andreas Gorzewski / Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman