Yarima Ben Salmane ya yi tir da kisan Khashoggi
October 24, 2018Ya sanar da hakan ne a wannan Laraba a gaban taron zuba jari da ke gudana a yanzu haka a birnin Riyadh. Wannan dai shi ne karo na farko da yarima ben Salmane ya yi tsokaci kan wannan lamari tun bayan kisan dan jaridar a karamn ofishin jakadancin Saudiyya da ke a birnin Istanbul na Turkiyya a ranar biyu ga wannan wata na Oktoba.
Sai dai kuma yariman ya bayyana cewa wannan hadari ba zai shafi huldar kasarsa da Turkiyya ba hasali ma za su yi aiki tare domin gano mutanen da suka aikata wannan danyen aiki domin gurfanar da su a gaban kuliya, kuma shari'a za ta yi aikinta
Da ma dai fadar Shugaban kasar ta Turkiyya ta sanar a wannan laraba cewa Shugaba Erdogan ya tattauna ta wayar tarho da Yarima Mohammed ben Salmane kan hanyoyin da ya kamata su bi wajen gano mutanen da suka aikata wannan danyen aiki.