1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden ya yi wa Kishida alkawarin kare Japan

Abdourazak Maila Ibrahim MAB
October 4, 2022

Shugaban Amirka Joe Biden da firayiministan Japan Fumio Kishida sun yin Allah wadai da matakin da koriya ta Arewa ta dauka na harba makami mai linzami a samaniyar Japan.

https://p.dw.com/p/4HjoV
USA Japan Biden Fumio Kishida Videokonferenz
Hoto: Cabinet Secretariat/Kyodo News via AP/picture alliance

Wata sanarwa da fadar mulki ta White House ta fitar ta ce shugabannin Amirka da Japan sun tattauna ta wayar tarho, inda Biden  ya sake tabbatar da yukurin Amirka na kare Japan. A daya hanun kuma, shugabannin biyu sun yi alkawarin ci gaba da yin magana da murya guda tare da Koriya ta Kudu a kan barazanar Koriya ta Arewa a duk lokacin da zarafi ya kama.

A wannan Talatar ce Koriya ta Arewa ta harba wani makami mai linzami mai cin matsakaicin zango a samaniyar kasar Japan, wanda ya kai Tokyo da neman mazauna wasu yankuna da abin ya shafa da su kaurace wa matsugunansu. Joe Biden da Fumio Kishida suka ce sun himmatu wajen takaita ikon Koriya ta Arewa na gudanar da shirinta na makami mai linzami ba bisa ka'ida ba.