1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden zai gana da shugaban Philippines

April 30, 2023

Shugaba Joe Biden na Amirka zai karbi bakuncin takwaransa na Philippines Ferdinand Marcos, a daidai lokacin da jiragen ruwan Philippines ke fuskantar barazana daga Chaina.

https://p.dw.com/p/4QjYU
Shugaban Philippines ya ziyarci sansanin gwajin rokaHoto: Ted Aljibe/AFP

Ziyarar ta Marcos a birnin Washington na zuwa ne bayan da kasashen biyu Amirka da Philippines ke shirin gudanar da atisayen hadin gwiwa na jiragen sama na yaki karo na farko tun daga shekarar 1990. A wannan shekarar ce, kasar Philippines ta amince wa Amirka damar samun karin sansanoni hudu a tsibirinta.

 Amirka na kokarin dakile barazanar Chaina ga Taiwan da kuma kudancin tekun Chinar da ake takaddama a kai. Shugaba Marcos ya ce yana sa ran kulla alaka mai karfi da Amirka domin tunkarar matsalolin da suke fuskanta a yanzu. Ziyarar shugaban na kasancewa ziyara ta farko da wani shugaban kasar Philippines ya kai Amirka cikin shekaru 10.