1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden ya samu izinin kara lafto wa Amirka bashi

June 3, 2023

Wata guda aka kwashe ana muhawara a kan bukatar kara yawan rancen da Amirka za ta ci bayan da ta kure gejin karshe na bashin da ya kamata ta karba, inda a makon nan sanatocin kasar suka amince da a kara karbo rancen.

https://p.dw.com/p/4S9K3
Hoto: Jim Watson/AFP/Getty Images

Shugaban Amirka Joe Biden ya ce zai rattaba hannu kan kudurin dokar da ke bukatar a kara yawan adadin kudaden da ya kamata gwamnatin kasar ta ciyo bashinsu. Biden ya ce zai dauki matakin hakan a wannan Asabar, yana mai cewa samun amincewar majalisar dattawan kasar a kan fadada kudaden da ya kamata su karbo rance, wani babban mataki ne da zai kawar da tattalin arzikin Amirka daga rugujewa.

Wata guda aka kwashe ana tabka muhawara a kan bukatar kara yawan rancen da Amirka za ta ci bayan da ta kure gejin karshe na bashin da ya kamata ta karba, inda a cikin makon nan mai karewa sanatocin kasar suka mince da kudurin dokar.

Duk da cewa kawo yanzu ba a sanar da adadin kudaden da kudurin dokar ya yi kari ba, amma a halin da ake ciki ana bin Amirka bashin da ya kai Dala tiriliyan 31, lamarin da 'yan majalisar jam'iyyar Republican da ke adawa suka ce ba abu ne mai kyau ga makomar kasar ba.