Bikin cikwan shekaru 60 da girka hukumar UNESCO
November 16, 2005Yau ne hukumar kulla da illimi, kimiyya da al´adu ta Majalisar Dinkin Dunia, wato UNESCO ke cika shekaru b60 daidai da girkuwa.
An kaddamar da shagulgullan a birnin Paris na kasar Fransa, inda shugaban hukumar Koichiro Matsura ya gabatar da jawabi.
Ya bayyana mahimman nasarorin da hukumar UNESCO ta cimma, a tsawon shekaru 60 na aiki.
Saidai a daya hannun ya nuna rashin gamsuwa a kan yadda, ya zuwa yanzu, hukumar ba ta cimma burin ta ba, na tabbatar da zaman lahia a dunia, ta la´akari da mace-mace masu yawa, dalili da bila´in yake yaken, da ke ci gaba, da barkewa a sassa daban daban na dunia.
Shugaban kasar Ukraine Viktor Iouchtenko, da ya halarci bukkunkunnan na birnin Paris, ya danganta burin UNESCO da na gwamnatin da ya ke jagoranta, ya kuma yi kira ga al´ummomin kasashen dunia, da su dauki sarar hakuri da juna, wadda ita ce hanya mafi a´alla ,ta shinfida zaman lahia a dunia.