Bikin Ista: Zomo a cikin fasaha
Jagora Dogon Kunne ba wai kawai mai samar da kwai na Ista bane. Zomo kuma sanannen samfuri ne ga masu fasaha.
Tina Oelker: Mai zanen Zomaye
Mai zanen Hamburg tana fentin zomaye ne a matsayin sana'a: izuwa shekarar 2021 ta zana zomaye 1000, duk a cikin salo daban-daban, kawai tsarin ya kasance iri daya. Wannan yana ba ta 'yancin yin gwaji na salo. Zomaye suna taka rawa a cikin dukkan al'adu, in ji Oelke. Ta takaita iliminta a matsayin kwararriyar zomo a cikin littafin "Von Hasen + Göttern 2001-2021".
Zanen Girkawa
Kurege ya riga ya shahara sosai a matsayin abin farauta a zamanin can baya. Amma dabbar ta kasance mai haihuwa, nau'in ya tsira. Saboda haka, an dauki zomo alama ce ta kuzari da sha'awar jima'i - halayen da aka sani a karni na 5 gabanin Annabi Isa. Hoton mu yana nuna wani mutum yana halartar taron karawa juna sani yayin da yake shafa zomo cikin mafarki.
Albrecht Dürer: Matashin Kurege
Dürers Aquarell daga 1502 ya shahara a duniya. Kuma ya kasance yana rataye a yawancin dakunan zama a Jamus. Na asalin yanzu, yana da gautsi kuma yana da kima wanda kawai ana nuna shi a cikin Albertinum na Vienna ko wace shekara biyar. Abin mamaki: A cikin binciken yanayi sama da shekaru 500, kurege dabba ce da kanta ba alamar addini ko tatsuniya ba.
Antonius: Zomo a makwancinsa
Ba kome ba ko kurege ne ko zomo: tun daga zamanin da na Girkanci zuwa yau, masu dogayen kunnuwa sun yi ado da zane-zane da sassaka. Mawakin hoto mai ruwa biyu Jamus da Amirke Antonius ya ci gaba da al'adar - tare da daukar hoto na zomo. Matukar dabi'a: Kuna iya ji a zahiri zomo na saka ciyawa yana shakarsa....
Zomo yana cin inibi
Tushen zomo na cin inibi ya shahara a wurin Romawa. Misali, yana wanzuwa a zaman zanen bango daga karni na 1 kuma a daga karni na 3. Wannan kafet din saka na 'yan Koftik ya samo asali ne a Masar a cikin karni na 6. Zomo yana cin 'ya'yan itace an yi niyya don cinye kansa. A bayyane ra'ayin ya kasance mai ban sha'awa.
Tagar zomaye uku
A cikin majami'ar Paderborn Cathedral za ku sami shahararriyar tagar zomaye uku, wanda ma'aikacin dutse ya sassaka a farkon karni na 16. Tushen zomaye uku sun riga sun wanzu a zamanin Romawa, misali a cikin nau'in fitulun mai. A cikin hotuna na mabiya addinin Katolika, hoton ya nuna "Kunnuwa uku" alama mai nasaba da Trinity.
Jeff Koons da zomonsa
Jeff Koons ya kirkira wannan sassaken karfe akan roba mai kyalli. Tana daya daga cikin gumaka na bayan zamani. Mawakin Ba'amirke ya kirkira su a cikin 1986 a matsayin wani bangare na jerin "Na doka", wadanda ke amfani da abubuwan yau da kullun. A cikin 2007, ya kãra wannan shirinsa zuwa cikin babban balloon, wanda aka ja ta cikin titunan New York don jawo hankalin jama'a.
Florentijn Hofman: Farar katuwar zomo
Kuma wani katon zomo. Hofman yana aika manyan dabbobinsa a duk fadin duniya. Ya wanke wannan zomo a rana a gundumar Taoyuan, Taiwan, a cikin 2014. Mawallafin dan Holland ba ya ganin hotunansa, wanda ya dogara da samfurorinsu, kamar dabbobi, amma a matsayin "zayyana kayan wasa". A karshe zomo - kyakkyawar alama ce ta sauki sarrafawa.
Mutum-mutumin Zomo
Zomo yana daya daga cikin shahararrun manufofin zanen tawada na gargajiya na kasar Chaina. Amma yawancin masu fasaha na zamani kuma sun yi maganin zomo. A cikin anguwar masu zane na 798 na birnin Beijing, mutum zai ga wannan mutum-mutumin zomo a cikin yanayi mai 'yanci da babbar girmamawar rayuwa.
Ai Weiwei: Zomon Zodiac
Zomo yana daya daga cikin alamun addinin Zodiac goma sha biyu na kasar Chaina kuma a shekarar 2023 ita ce shekarar zomo. Hoton tagulla na Ai Weiwei yana nufin tarihin musanya tsakanin Turai da Chaina. Ya kwaikwayi wani karamin kwanyar da kiristoci biyu suka kirkira wa sarkin Chaina a karni na 18. Bayan shekaru dari, sojojin Birtaniya sun sace shi da wasu kawunan dabbobi goma sha daya.