Zagayowar bikin Maulidi
December 11, 2018Birnin Damagaram na jamhuriyar Nijar na daga cikin garuruwan da al'ummar Musulmi ta gudanar da wannan biki kuma, Cheik Imam malam Amadu mai wa'azi daya daga cikin jagororin Musulmi a birnin na Damagarm ya yi bayani a game da fa'idar wannan biki na tunawa da ranar haifuwar manzon rahama. Tsohon shugaban kasar Nijar Alhaji Mahaman Usman da kansa ya ja karatun littafiyar ishriniya a ranar babban daren. Dubban Musulmi ne maza da mata da yara dai suka halarci masallatai da zawiyoyin da ke shirya tarukan maulidin a birnin na Damagaram. A makobciyar kasar ta Nijar ma dai cewa da Tarayyar Najeriya Musulmi sun raya babban daren a garuruwa da dama. Birnin Bauchi na daga cikin biranen da aka gudanar da wannan biki na maulidi kuma Sheik Kabir Al-Arabi Bauchi daya daga cikin shugabannin darikar Tijjaniya a garin na Bauchi ya yi bayani a game da tarihin kafuwar bukukuwan maulidin a cikin al'ummar Musulmi.