Bikin ranar abinci ta duniya ya zo da matsaloli
October 17, 2014Ko wace ranar 16 ga watan Oktoba ne dai MDD ta ware, domin yin dubi kan wadata al'umma da abinci, amma a bana bikin ya samu wasu wurare irin arewacin Najeriya cikin matsalolin tsaro. Lamarin da ake ciki ya yi sanadiyyar gujewa gonaki, inda manoma da dama suka tsere daga gidajensu, sakamakon tashin hankali da ake fiskanta musamman inda kungiyar Boko Haram ta karbe iko da garuwa da dama.
Bugu da kari akasarin inda ake tashin hankali wurare ne da ake da manoma wadanda ke wadata jama'arsu da abinci, kasancewar babu abinda aka dogara da shi a rayuwar yankin in banda noma. Sai dai kaito rikicin ya yi kamari ne a lokacin da yabanyar gonaki ke kan tashi. Don haka masana suka yi kiyasin cewa, rashin zaman lafiya da ya haddasa dubban manoma suka tsere bisa tsira da rayukansu, kuma hakan zai haddasa karancin abinci a fadin kasar ta Najeriya da makobtanta.
A jamhuriyyar Nijar ma Hukumar kula da abinci ta duniya wato FAO rashen kasar, ta gudanar da taron manema labarai, inda ta bada sakamakon halin da ake ciki na yanayin ci-maka a kasar. Jamhuriyar Nijar dai ta yi suna bisa fiskantar matsalolin ci-maka, inda a wasu shekarun aka yi ta fama da matsalar tamowa. A nasu wajen su ma kungiyoyin farar hulla a Nijar, sun shirya wata mahawara kan matsalar abinci a kasar. A jamhuriyar ta Nijar dai a bana damina ta zo da tanganrda a wasu yankunan kasar, inda damina bata yi yadda ake zato ba.
Wata babbar matsala da ta fi shafar harkar noma a kasashe musamman kudu da Sahara, ita ce batun sauyin yanayi, inda ake samun karuwar korarowar Hamada.