1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin ranar zagayowar harin nukiliyar Japan

August 6, 2012

A litinin din nan (06.08.12) ce ake gudanar da bikin zagayowar ranar da aka jefa bama-baman nukiliya a garin Hiroshima da ke ƙasar Japan shekaru sittin da bakwai da su ka gabata.

https://p.dw.com/p/15kT4
Japan Atombombe HiroshimaHoto: AP

Wani jirgin yakin Amirka kirar B-29 da a ka yi wa laƙabi da 'Enola Gay' ne ya jefa bam din nukiliyar a garin na Hiroshma a shekarar 1945 inda ya lalata mafi akasarin garin tare da sanadiyyar rasuwar mutanen da yawansu ya kai dubu ɗari da arba'in, kwanaki kalilan kafin ƙarshen yaƙin duniya na biyu.

Kwanaki uku bayan jefa bam ɗin da aka yi a Hiroshima, har wa yau an sake jefa wani a garin Nagasaki wanda shi ma ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama.

Kimanin mutane dubu hamsin ne ke hallartar bikin na yau, yayin da waɗanda su ka tsira da rayukansu lokacin da aka jefa bama-baman na Hiroshima da Nagasaki da kuma wadanda su ka tsira daga bala'in nukiliyar Fukushima na shekarar da ta gabata ke gudanar da zanga-zanga domin nuna adawarsu da amfani da makamashi na nukiliya saboda abin da su ka kira haɗarin da ke tattare da shi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh