1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bincike kan hari a Indiya

July 14, 2011

Mahukunata a ƙasar Indiya sun ƙaddamar da bincike domin gano waɗanda ke da alhakin harin da aka kai a birnin Mumbai a ranar 13 ga watan Yuli

https://p.dw.com/p/11uw5
'Yan sanda da jami'an kwantar da tarzoma a inda hari ya auku a birnin MumbaiHoto: dapd

A ƙasar Indiya ana nan ana gudanar da bincike akan hare-haren bom da aka aiwaitar ranar Laraba 13 ga watan Yuli da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 17. Komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi Allah wadar da hare haren da aka ƙaddamar a wata cibiyar kasuwanci da ke kudancin birnin Mumbai. Wasu kuma su 40 sun samu raunuka. Shekaru biyu da rabi kenan da wasu 'yan bindiga da ake zaton daga Pakistan suka fito suka aiwatar da hare-hare a wannan wuri. Babu dai wata ƙungiya da ta yi iƙirarin kai wannan hari. Amma ministan cikin gidan Indiya ya faɗa wa manema labarai cewar 'yan ta'adda ne ke da alhakin wannan hari.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu