Bincike kan harin iyakar Turkiyya da Siriya
May 14, 2013Talla
Ministan yada labaran Siriya Omran al-Zohbi ne ya shaidawa manema labari hakan a wannan Talatar inda ya ce gwamnatin Assad shirye ta ke da ta ga an gudanar da bincike kan harin domin tantance hakikanin wanda su ka kai shi.
A ranar Lahadin da ta gabata ce dai wasu 'yan kunar bakin wake su ka kai harin na garin na Reyhanli wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama, harin da hukumomin Turkiyya su ka ce wasu mutane da ke alaka da hukumar leken asirin Siriya ne su ka kai shi bayan da su ka ce sun kama mutane tara da su ke zargi da kai harin, zargin da Siriya ta musanta.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh