1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bincike kan turereniya a Kenya

October 24, 2010

Firaministan Kenya ya ba da umarnin gudanar da bincike kan turereniyar da ta halaka mutane bakwai a Nairobi

https://p.dw.com/p/PmXz
Hoto: picture-alliance/ dpa

Firaministan ƙasar Kenya Raila Odinga ya ba da sanarwar gudanar da bincike dangane da turereniyar nan da ta yi sanadiyar mutuwar mutane bakwai dake ƙoƙarin shiga filin wasan ƙwallon ƙafa a birnin Nairobi. Ma'aikatan ceto a babban birnin na Kenya sun ce aƙalla mutane 20 masu sha'awar ƙwallon ƙafa suka samu raunuka sakamakon turereniyar wadda ta auku lokacin da 'yan kallo da ba su da katin shiga filin wasa suka yi ƙoƙarin shiga filin wasa na Nyayo domin kallon karawa tsakanin ƙungiyoyin Gor Mahia da AFC Leopard a jiya Asabar. Firaminista Raila Odinga ya ce za a gudanar da bincike tsakani da Allah kan wannan lamari.

Ya ce: "Mun bawa 'yan sanda umarnin gudanar da bincike nan-take akan jami'ai waɗanda alhakin shirya wasan ƙwallon ƙafa ya rataya a wuyansu wato ma'aikatar wasanni. Za a gudanar da bincike sosai domin mu gano musabbabin aukuwar wannan turereniya."

Waɗanda suka shaida abin da ya faru da kuma likitoci masu ba da taimakon gaggawa sun ce aƙalla mutum ɗaya wato wata matashiya ta mutu sakamakon raunin da ta samu saboda rashin isowar taimako da wuri. To sai dai wani babban likita a wurin ya ce cunƙoson mutane sun toshe hanyoyin shiga filin wasan abin da ya kawo ciƙas ga motocin ambulans na ɗaukar marasa lafiya kaiwa ga masu buƙatar taimako.

A shekarar 2005 lokacin wasan fid da ƙasashen da za su kara a wasannin cin kofin ƙwallon ƙafa, an take mutum ɗaya har lahira a wata turereniya da ta auku a wannan filin wasan.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi