Binciken amfani da makamai masu guba a Siriya
September 16, 2013Masu bincike na Majalsar Dinkin Duniya sun bayyana cewar, babu ko shakka game da amfani da makamai masu guba a rikicin Siriya, yayin wani harin da ya janyo mutuwar daruruwan jama'a a watan jiya, domin kuwa suna da hujjoin da ke tabbatar da hakan. Rahoton da masu binciken suka gabatar wa sakataren majali, ya ce binciken da suka gudanar a yankunan da matsalar ta fku, da sinadaran da suka tatttaro, game da asibitocin da suka ziyarta, sun tabbatar musu da cewar, an yi amfani da makamai masu guba a yankin Ghouta da ke wajen Damascus, babban birnin kasar a ranar 21 ga watan Agustan da ya gabata. Kmfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewar, abin da binciken ya gano kawai shi ne cewar, an yi amfani da makamai masu guba a yakin da ke ci gaba da wanzuwa a tsakanin sassan da ke ckin rikicin na Siriya, a kan fararen hular da suka hada da kananan yara da mata. A dai wannan Litinin ce sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon, wanda tuni ya karbi rahoton, zai gabatar dashi ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal