Binciken Trump: Fiona Hill ta fasa kwai
November 22, 2019Talla
Tsohuwar jami'a a fadar shugaban Amirka Fiona Hill ta fasa kwai yayin da ta ke bada ba'asi a cigaba da binciken tsige shugaba Donald Trump.
Hill ta shaidawa kwamitin binciken cewa babban jakadan Amirka a tarayyar Turai Gordon Sondland tamkar dan koren gida ne wanda aka sanya aike domin bin diddigin 'yan Demokrats. Wannan bayani dai ya bada mamaki da kuma sage gwiwar masu kare shugaba Trump a kwamitin binciken.
Bugu da kari Fiona Hill ta kuma bukaci yan Republican da shi kansa shugaba Trump da cewa su daina yaudarar al'umma ta ce an bar jaki ana duka taiki, Rasha ita ce ta yi wa Amirka kutse a zaben 2016 amma ba Ukraine ba.