Birtaniya ta kafa dokar hana zirga-zirga
March 24, 2020Talla
Birtaniya ta bi sahun wasu kasashen duniya da suka kafa dokar hana zirga-zirga, har na tsawon makonni uku, a kokarin ganin sun dakile yaduwar annobar coronavirus.
Wannan sanarwar na zuwa ne bayan gargadin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi game da karuwar wadanda cutar take kamawa a duniya.
Da ya ke jawabi ga al'ummar kasar, Firaminista Boris Johnson ya umurci a rufe dukkan shaguna in ban da na kayan abinci da kuma sayar da magunguna.