Shekaru 40 da murabus din Ahidjo na Kamaru
November 4, 2022Talla
Shi dai Biya mai shekaru 89 da haihuwa ya zama daya daga cikin shugabanni mafi dadewa a mulki a duniya, godiya ga mukarrabansa da ke rike da manyan mukamai.
Bayan shekaru bakwai na zama firaminista, Biya ya hau karagar mulki a ranar shida ga Nuwamban 1982, inda ya kasance shugaban kasa na biyu tun bayan da Kamaru ta samu 'yancin kai a 1960.
Rigingimun siyasa da zamantakewa ta rashin tsaro na daga cikin matsalolin da suka dabaibaye tsarin mulkinsa na sai madi-ka-ture, daura da matsaloli na tattalin arziki.
Tun bayan faduwar Robert Mugabe a shekarar 2017, Biya ya zama shugaban Afrika mafi tsufa kuma na byu mafi dadewa a kan mulki bayan na Equitorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo.