Blinken: Dama ta karshe ta cimma sulhu a Gaza
August 19, 2024Blinken wanda ya kai ziyara karo na tara a yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan harin da Hamas ta kai harin ranar 7 ga watan Oktoba da ya haifar da yakin Gaza, ya ce ya koma Israila domin ganin an kai gaci wajen cimma yarjejeniya da kuma kawo karshen yakin.
Yana mai cewa wannan lokaci ne mai muhimmanci, mai yiwuwa mafi dacewa, watakila ma dama ta karshe ta dawo da mutanen da aka garkuwa da su da samun tsagaita wuta da kuma dora kowa akan tafarkin zaman lafiya mai dorewa.
Sakataren harkokin wajen na Amurka ya kuma gana da Firaministan Israila Benjamin Netanyaahu a birnin Kudus sannan a ranar Talata zai wuce zuwa Masar inda ake sa ran ci gaba da tattaunawar tsagaita wutar a wannan makon.
An dai shafe watanni ana kai komo wajen tattaunawar da mashawarta daga Amurka da Qatar da kuma Masar suke shiga tsakani ba tare da cimma yarjejeniyar ba.