1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin inganta dangantakar Amurka da Saudiyya

Ramatu Garba Baba
June 6, 2023

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, zai yi wata ganawa ta musanman da Yarima Muhammad Bin Salman a yayin ziyararsa a Saudiyya.

https://p.dw.com/p/4SEko
Sakatare Antony Blinken a yayin wata ganawa da Yarima Faisal Bin Farhan Al Saud
Sakatare Antony Blinken a yayin wata ganawa da Yarima Faisal Bin Farhan Al SaudHoto: Jonathan Ernst/AP Photo/picture alliance

A wannan Talata, Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, zai kai wata ziyarar aiki a kasar Saudiyya, ziyara da ake wa kallon a matsayin kokarin inganta dangantaka a tsakanin kasashen biyu bayan rashin jituwa kan batutuwa da dama.

Sai dai kafin soma ziyarar ta Blinken, jaridar The New York Times da ake wallafawa a kasar Amurka ta ruwaito cewa, Yarima Muhammad Bin Salman mai jiran gadon sarautar Saudiyyan, ya nemi Amurka ta ginawa kasarsa tashar makamashin Nukiliya a madadin kulla cikkakiyar hulda da Isra'ila, lamarin da Amurkan ke ci gaba da nazari a kai.