1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dole a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasa a Brazil

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
October 3, 2022

Shugaba Jair Bolsonaro da Luiz Inacio Lula da Silva na zawarcin jam'iyyun siyasa a Brazil a yayin da ake dakon zagaye na biyu a zaben shugaban kasa a karshen watan Oktoba.

https://p.dw.com/p/4HgHl
Wahlkampf Brasilien I Bildkombo Bolsonaro und Lula
Hoto: AFP

Shugaba Jair Bolsonaro da abokin hamayyarsa mai ra'ayin kawo sauyi Luiz Inacio Lula da Silva za su fafata a zagaye na biyu na zaben shugabancin Brazil a karshen wannan wata, bayan kowannen su ya kasa samun gagrumin rinjayen da ake bukata don lashe zabe a zagayen farko.

Da dama na ganin shugaba Bolsobnaro da ke neman karin wa'adin mulki ya yi ba za ta, duba da yadda sakamakon kuri'ar jan ra'ayin jama'a ya nuna abokin hamayarsa Lula da Silva ka iya lashe zaben tun a zagayen farko ba tare da wani shamaki ba.

Tuni ma dai da Silva ya ambaci fara gangamin yakin neman zabensa a karo na biyu a wannan Litinin. Sai dai kuma yana ci gaba da shan suka daga abokin hamayarsa Jair Bolsonaro, wanda ya bayyana shirin Luiz Inacio Lula da Silva a matsayin mai hadari da ka iya kawo Brazil gagarumin koma-baya.