Boren adawa da gwamnatin Saudiyya
July 27, 2012A ƙasar Saudiyya jam'ian tsaro sun kama ɗaruruwan jama'a da suka shiga boren neman sauyi. Kamfanin dillalcin labaren ƙasar yace boren ya farune a gabacin ƙasar inda ma biya ɗariƙar Shi'a suka fi ƙarfi. Wadanda da suka yi bore a yau Juma'a kana sun yi ta ƙona taoyoyi, kafin jam'an tsaro su fatattakesu. Ƙasar Saudiyya dai kamar sauran ƙasashen Larabawa an jima ana boren neman kafa mulkin demokraɗiyya, amma ba da safai labarin yake fitowa ba a kafafen yaɗa labaraen duniya. Rahotanni sun jiyo kakakin ma'aikatar cikin gidan Saudiyya na mai cewa, mutanen da aka kama sune ke ingiza wutar boren adawa da gwamnati da ake yi tu bara, inda yace waɗanan masu boren da aka dade ana yinsa aksari yan Shi'a ne marasa rinjaye, inda suke neman gwamnati Saudiyya ta yi musu adalci. Saudiyya dai ita ce kanwa uwar gami, wajen neman sai a tallafawa yan tawaye dake neman akafa mulkin ɗemokradiyya a ƙasar Siriya, kuma ta na daga cikin masu tallafawa yan tawaye dake neman kifar da gwamnati Bashar Al-Assad.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Zainab Mohammed Abubakar