Boren masu rajin kare muhalli a Turkiya
June 1, 2013'Yan sandan kasar Turkiya sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi, kan masu zanga-zanga a birnin Santanbul, abin da ya janyo jikata mutane masu yawa, kuma yanzu haka wannan zanga-zanga ta bazu zuwa wasu biranen kasar da suka hada da Ankara babban birnin kasar da garin Izmir mai tashar jiragen ruwa. Zanga-zangar ta Santanbul ta samo asali ne, saboda nuna adawa da sare bishiyoyi 600 a wurin shakatawa na birnin, domin gina manyan shaguna. Tuni ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta Turkiya, ta ce za ta binciki zargin amfani fiye da karfi da 'yan sanda suka yi. Kamar yadda 'yan sanda suka nunar an kame mutane fiye da 60 wadanda suka shiga zanga-zangar ta neman kare wurin shakatawa na Gezi-Parks inda ake shirin wani gagarumin aikin gine-gine. A wasu wuraren zanga-zangar ta rikide zuwa boren kin jinin manufofin gwamnatin Firaministan Recep Tayyip Erdogan mai ra'ayin mazan jiya.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal