Coronavirus: Boris Johnson ya killace kansa
March 27, 2020Talla
Boris Johnson ya ce ya fara jin zazzabi kana yana tari ya ce bisa umarnin likitocinsa ya yi gwajin cutar Coronavirus kuma aka ce ya kamu da ita. Boris din ya ce ya killace kansa amma dai yana ci gaba da jagorantar harkokin gudanarwa na mulki. Sannan maidakinsa wacce ke da juna biyu an wareta daga gidan na iyali kamar yadda gwamnatin ta bayar da umarni.