1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buga gangar yaki a yankin Koriya

Usman Shehu Usman
April 17, 2017

Kasashen Rasha da Koriya ta Arewa da Amirka suna yarfa wa juna kalaman da ke barazanar barkewar yaki, bisa abin da ya shafi mallakar makamai a Pyongyang

https://p.dw.com/p/2bMaZ
Nordkorea Kim Jong Un besucht militärischen Wettbewerb
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Sinmun

Jakadan Koriya ta Arewa a MDD Kim In Ryong, ya fadawa manema labarai cewa, idan fa kasar Amirka ta kuskura ta gwada yin amfani da karfin soja, to Koriya ta Arewa ba za ta bata lokaci ba, don mayarda dukkan martani irin na yaki, wanda zai iya dacewa da kasa kamar Amirka. Ofishin jakadancin Koriya da ke MDD ya mayarda martani ne bayan mataimakin shugaban kasar Amirka Mike Pence, ya ziyarci rundunar sojan kasar da ke gabar ruwan Koriya, inda Pence  ya fada cewa kada fa Koriya ta Arewa ta gwada fushin Amirka.

            Gargadi daga Rasha

Hukumomi a Rasha sun gargadi Amirka kan kaddamar da hari a Koriya ta arewa, bayan kalaman mataimakin shugaban Amirka Mike Pence da ke nunin cewa saurarawa Pyongyang kan makami mai guba ya riga ya wuce. Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya ce wannan hatsari ne mai girman gaske.

A wani taron da aka yi da 'yan jaridu a wannan Litinin a birnin Moscow, Rashar ta ce bata amince da yin gaban kai da Koriya ta Arewar ke kokarin yi ba, sai dai kuma hakan ba zai zamo hujja ta karya doka irin wanda aka gani a Syria a 'yan kwanankin nan ba.

Gwamnatin Rashar ta kuma gargadi Koriya ta Arewa da kada ta amince wa shugaba Trump, yin abin da yake fata, maimakon hakan kamata ya yi a sulhunta kan maganar muggan makaman na kare dangi.