1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya goyi bayan sauya fasalin Naira

October 31, 2022

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya goyi bayan sauya fasalin wasu takardun kudi da babban bankin kasar, CBN, ke shirin aiwatarwa, yana mai cewa matakin ba zai cutar da duk wanda ya samu kudi ta halastacciyar hanya ba.

https://p.dw.com/p/4Irx5
Shugaba Muhammadu Buhari na NajeriyaHoto: DW/I. U. Jaalo

Buhari ya fadi haka ne a wata hira da ya yi da wani gidan talabijin a Najeriya mai suna Tambarin Hausa TV, shugaban ya ce mutanen da ke da dukiya ta haramun ne kadai za su yi fargaba a kan wa'adin da CBN ya bayar domin musayar kudin yana mai jaddada cewa matakin ba zai cutar da 'yan kasuwa da ma'aikata masu neman halaliya ba. A makon da ya gabata ne shugaban bankin na CBN Godwin Emefiele ya ce kimanin takardun kudi na Naira tiriliyan biyu da biliyan 700 cikin Naira tiriliyan uku da biliyan 300 da gwamnati ta san da zamansu ne ke jibge a gidajen mutane ba tare da sun ajiye su a bankin ba, lamarin da ya ce na cutar da tattalin arzikin kasar. A kan haka ne ma Babban Bankin na Najeriya ya kuduri aniyar sauya fasalin takardun kudin da suka hada da Naira 200 da 500 da kuma 1000.