October 8, 2018
Talla
Nasarar da tsohon mataimakin shugaban Najeriyar Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ta ‘yan adawa ya samu, bayan da ya kayar da mutane 11 da suka yi takara, ya nuna cewar shi ne ke kalubalantar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC mai mulki. Wannan ya bude sabon babi a guguwar siyasar da ke kadawa, domin kar-ta- san- kar a tsakanin mutanen guda biyu.
Dr Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja ya bayyana hasashensa ga irin fafatawar da za'a yi, inda ya ce " Za'a yi fafatawa mai zafin gaske ganin cewar Atiku Abubakar hamshakin dan siyasa ne da kuma wanda yake yi wa adawa shugaban kasa da ke rike da madafun iko.