1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Girmama hakkin 'yan jarida

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 25, 2023

Masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai a Afirka, sun yi kira ga gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar da ta girmamam hakkin 'yan jarida.

https://p.dw.com/p/4VaPl
Nijar | Janaral Abdourahmane Tiani | Juyin Mulki | 'Yanci | 'Yan Jarida
Jagoran juyin mulkin sojan Nijar Janaral Abdourahmane TianiHoto: Balima Boureima/Reuters

Kungiyar 'Yan Jarida na Gari na Kowa wato RSF ce ta yi wannan kiran, inda ta ce ta shirya wani gangami na wasu mutane 80 da suka hadar da mamallaka kafafen yada labarai a kasashe rainon Faransa. Cikin wata sanarwa da kungiyar ta RSF ta fitar, ta bukaci jagororin juyin mulkin na Nijar da su girmama 'yancin samun bayanai da na zaman tare da ma 'yancin kafafen yada labarai. Ta kuma yi kira ga sojojin da su taimaka wajen tabbatar da kariya ga 'yan jarida na gida da na kasashen ketare. Kungiyar ta RSF ta ce ta yi wannan sanarwar biyo bayan afkuwar wasu al'amura, tana mai cewa take hakkin 'yan jarida ya karu matuka a Jamhuriyar ta Nijar tun bayan juyin mulkin.