Bukatar samar da gagarumin shirin taimaka wa 'yan Siriya
December 18, 2014Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin tarayyar Jamus sun nuna bukatar samar da karin taimako na tsawon shekaru masu yawa da nufin magance kwararar 'yan gudun hijira daga rikicin Siriya. Wani daftarin shirin gaggawa da wasu hukumomi uku na Majalisar Dinkin Duniya da kawayensu suka gabatar a birnin Berlin ya ce ana bukatar Euro miliyan dubu 8.4 wajen taimaka wa 'yan Siriya su kimanin miliyan 18 da suka tsere zuwa wasu yankuna na kasar da kuma kasashe makwabta. Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce abin da aka sa gaba shi ne samar da wasu ginshikai na dogon lokaci. Valerie Amos da ke zama mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a kan al'amuran jin kai cewa ta yi ba za a tsaya ga ba wa mutane abinci da tufafi da kuma muhalli kadai ba.
Ta ce: "Dole ne mu san cewa mutanen suna son su ci gaba da tafiyar da rayuwarsu. Dole mu san irin tasirin da kwararar 'yan gudun hijira ya yi a kan tattalin arziki da sauran abubuwan more rayuwa a kasashe makwabta da suka nemi mafaka cikinsu."