Shekaru 71 da da harin Amirka a Japan
August 15, 2016Talla
A ranar 15 ga watan Agustan shekara ta 1945 ne dai Amirka ta kai wasu tagwayen hare-haren nukiliya a biranen Hiroshima da Nagasaki na kasar ta Japan, sarkin kasar na wancan lokaci Hirohito ya fito ya yi jawabin mika wuya kasarsa a wannan yaki. Da ya ke jawabi a gurin taron tunawa da wannan rana, Sarki Akihito mai shekaru 82 a duniya wanda kuma da ne ga tsohon sarkin marigayi Hirohito, ya bayyana cewa yana takaici idan ya waiwayi tarihin abin da ya wakana a baya, inda ya ce yana fatan yaki irin wannan ba zai kara afkuwa a nan gaba ba. Mutane sama da miliya uku ne dai da suka hadar da sojoji da fararen hula a kasar ta Japan, suka rasa rayukansu a yayin yakin duniyar na biyu.