1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkin Faso: Binciken kisan wasu 'yan Najeriya

Binta Aliyu Zurmi
February 7, 2023

Mahukunta a Burkina Faso sun sanar da fara bincike a kan zargin da ake yi wa dakarun sojinsu na kisan wasu 'yan Najeriya da ke kan hanyar su ta zuwa birnin Kaolaha na kasar Senegal.

https://p.dw.com/p/4NAt8
Burkina Faso | Soldaten
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

A ganawarta da jakadan Najeriya a kasar Misitura Abdulraheem, minista harkokin wajen Burkina Faso Olivia Roumba ta tabbatar da bude babin sahihin bincike a kan wannan zargi, sai dai ta ce ya zuwa yanzu babu wasu kwararan bayannai ko shaidu da ke alkanta sojojin nasu kai tsaye da wannan zargi.

Mahukuntan na Ouagadogou dai tun bayan da kafafen yada labarai a Najeriya suka fidda wannan labarin, sunmusanta da ma kin amincewa da shi.

Burkina Faso na daya daga cikin kasashen da ke yammacin Afirka da ke fama da ayyukan mayakan da ke ikirarin jihadi, dubban jami'an tsaro da na fararen hula ne suka rasa rayukansu a hare-haren kasar da dama a kasar, yayin da sama da wasu da dama sun rasa matsugunnansu.