1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina: Gwamnati ta dakatar da watsa France 24

March 28, 2023

Gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ta dakatar da watsa shirye-shiryen gidan talabijin din kasar Fasansa mai lakabi da France 24 a duk fadin kasar.

https://p.dw.com/p/4PNlV
Shugaban gwamnatin Sojan Burkina Faso | Cap. Ibrahim TraoreHoto: AA/picture alliance

Gwamnatin ta Kyaftin Ibrahim Traore ta ce ta dauki wannan mataki ne bayan wata hira da gidan talabijin din ya yi da wanni shugaban kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Qaida da ke da'awa da makamai yau da 'yan shekaru a yankin Sahel tare kuma da hana al'ummomin yankin sukuni.

Gwamnatin ta Burkina Faso ta kara da cewa yin hira da 'yan ta'adda a kafar talabijin din tamkar tallata aikin ta'addaci ne sannan kuma ko kadan ba za ta lamince ba wata kafar sadarwa ta kasar waje ta ringa yada kalamai na kiyaya da tsautsaran ra'ayayi, domin kalamai ne da ka iya yin tasiri a gurin 'yan kasar.

Matakin da ke zuwa bayan korar sojojin Faransa daga Burkina Faso shi ne irinsa na biyu da gwamnatin sojan kasar ke dakatar da watsa shirye-shiryen kafafen sadarwar Faransa domin ko da a shekar bara sun dauki irin wannan mataki kan gidan radiyon RFi kuma hakan na nuna cewa Burkina Fason ta bi sahun makwafciyarta Mali wacce tun ba yau ba ta dakatar da watsa shirye-shiryen wadannan kafafe biyu.