Ta'addanci
Shawo kan matsalar tsaro a Burkina Faso
May 13, 2023Talla
Majalisar dokokin rikon kwaryar ta Burkina Fason ce ta amince da wannan kudiri ba tare da hamayya ba, inda a yanzu dokar ta-bacin za ta kawo karshe a ranar 29 ga watan Oktabar bana. Ministar shari'a na kasar Bibata Nebie Ouedraogo ta bayyana cewa, dokar ta-bacin za ta taimaka gaya wajen shawo kan matsalar tsaro da kuma bai wa jami'an tsaro damar yin aiki tukuru. Dokar da gwamnati ta sanya a watan Maris na wannan shekara, an yi ta ne domin taimakon jami'an tsaro musamman a binciken gida-gida da suke yi dare da rana domin gano bata-gari da kuma takaita zirga-zirga da taruwar jama'a.